Thursday, November 6, 2008

Wakar Talauci da Wadata; Darho

Al'adal Hausawa su kan rena matsiyaci, su kan yaba mai-dukiya,
suna rena baba matsiyaci, suna yaba yaro mai-kurdi, don haka
wani mutum ya wake halin Hausawa duka, sunansa Darho. Ita ke
nan :

A wannan waka, za'a ga anyi amfani da Hausa mai tsauri, domin kuwa, wannan tsohuwar waka ce. An rubuta ta ba tun yau ba. Ita ma na cikin wakokin da Malam Umar Salga ya baiwa Mischlisch a Kumasi.

1 Muna soma waka da suna na Allah,
Gama za mu tsari na halin tsiya .

2 Muna son kidaya t a halin talauci
Da halin wadata f a don ku jiya .

3 Kamannun talauci baki ne gajere
Da doro da tura da annakiya.

4 Kadan yabi yaro, shi tsofas dashi ,
Shi tantakore shi , shi yi kaman kugiya.

5 Idan ya bi tsofo, shi kan Rarasa shi ,
Shi rame, shi komo kaman tsarkiya .

6 Mutum mai-nagarta, kadan ya talauta ,
A maishe shi mugun, da ba gaskiya.

7 Mutum mai-karimci, kadan ya talauta ,
A ce, bashi kyauta da ko kokiiya.

8 Talakan mutum ba shi zance a taro ,
Fa zancensa sai ko cikin zuciya.

9 Kadan ya yi,zance a kan gaskiyarsa,
A ce masa, karya ka kai mun kiya.

A lalata zancen, a yaryamutsa shi ,
A maishe shi wauta abin dariya .

Fa baba talaka a maishe shi yaro,
A ce masa gebe kaman saniya .

Ace masa raggo, ace bashi lura ,
Ace masa, baban da ba moriya.

Kadan anyi taron buki, baa sa shi ,
Fasai za a watse, a kan tambaya.

Kadan za a taro na suna da amre,
Fa sai anyi nisa , a ce, shiyi biya.

Kadan an yi t aro , kamalsa daban ce,
Da wandonsa tsofo da 'yar Z ariya .

Fushin mai talauci abin dariya ne,
Fushinsa da murnalsa duka dai daya.

Talakan mutum ba shi samun aboki,
Fa wa ke abuta da dan shegiya?

18 Fa mai son talaka f a Allah Ta’alah,
Da ya y i talaka cikin jar wuya.

Fa mugun hali duk shi na gun talaka ,
Kadan dai ana son fadin gaskiya.

kazamta da wauta da bata zumunta
Da rowa da ka r ya da aikin riya .

A mugun jini babu tamkar talaka
Gidan duniyan nana ko mu jiya .

Idan ya y i zance da fara 'a ace mai,
dumi a gare shi cakoikoiniya.

Idan ya y i kawaici, a ce masa
Mugu da keta gare shi cikin zuciya.

Ka san, ba nagarta ga mai-yin talauci ,
Kadan za shi zance, a kan ce: tsaya .

Da zancenka mugu na wofi a duniya,
Zama ba ka zancen, da za’a biya .

Fa dangin talaka su nai masa kushe,
Su ce masa zumu ne, da ba moriya.

Ayyukan talaka dadai ba su kyawu
Ga bakin mutane f a har zuciya.

Idan yai da zaf i , su ce, babu tsabta ,
Yana tsarmatawa ga aiki jiya .

Idan yai da kyawu su ce, babu samri,
Yana da nawa, ya ki yi tun j i y a .

Yawan dariya gun talaka , mutane
Su maishe shi wawa kaman kanikiya .

Idan ya y i kawaici, su ce masa, mugu,
Cikinsa da zurfi kaman tumniya.

Fa inda talauci mutum ne, mutane,
Muna damre mu kekewaya.

Mu j e har bugensa, mu far masa da yaiki,
Mu ci shi , mu kamai, mu sa karkiya .

Mu ti kai mu kayes, mu damre, mu yanka,
Mu ja shi , mu yes can, mu ba maikiya.

35 Fa inda haki ne, muna ciccireshi ,
Shi bushe mu tara mu kone tsiya .

Fa haja ta talaka dadai ba ta kyawu,
Zuma nai a kan ce kaman tsamiya.

Idan yakuwa ce a kan ce da tsami,
Madi nai akance da kunkunniya.

diya tai dadai ba t a kyawu ga kowa,
A kan ce, gajera1 ga mai-cibiya.


Da kai gurgurrare, dada ga kumatu
Kaman diya ne na tumfaf iya.

Da cassa da ganni da kwarfin idanu
Da bakinta dogo kaman tsishiya .

A ce mata da kirci dada babu zama
Da warin jiki , sai ka ce rajiya .

Idan t a f i kyawu, a kan ce, da tsiwa,
Fa bata da kumya kaman shegiya.

Mutane, talauci mu ki shi da gaske,
Zama da talauci shina da wuya.

Idan an y i yunwa, abincin talaka
Fa ganyen rama, dorawa, gasaya.

Da rogo, da taura, da gaude, da tsada '
Da dumya da tafasa da har rojiya .

Da faru da gudai, kadanya, tamaka,
Dada magoraza, ciwo kinciya.

Talaka ana kinta amre gaduniya,
A sa mata aibu a rarrataya .

A ce mata kazama, tana barka zana,
A ce, bata shara f a , babu roriya .

Idan malami yai talauci ya shuda,
A kan ce, tababben ga nan ya biya.

A kan ce, karatunsa ya f irgita shi ,
A maishe shi wawa, abin dariya.

Idan yayi zance da nassi , a kyale,
Idan yayi harda, ace, ku jiya .


52 Fa ya tuna haukansa yau tun da s a f e ,
Makoftasu kan ce, fa ai tun jiya . "

Diya ta talaka idan baka ce,
A kan ce, bakinta da muni, jiya .

Idan kuwa, f arace ace tayi muni,
Farin ya faye, sai ka ce zabiya.

Idan tai gajerta ace babu kyawu,
A ce, dunkulalla kaman makaya.

Idan doguwa ce, akan ce, fatalwa,
Tsawon ya faye, kai , abin da wuya.

Dada kun ji halin talauci ku l u r a ,
Ku kilshe , ku tashi bidal dukiya.

Ku shirga Safara, ka j e har Fatoma,
Ku komo t a Bobo, ku zo Daboya.

Ku juya t a Jije , ku juyo ta Dor i
Ku jirgo ta Moshi ku zo har Kaya

Ku komo t a Salaga, ku j e har Kumashi,
Ku zaga t a Guwa, har Agaya.

Ku j e har Kano babu nisa wuce can,
Wadai kuma ka komo Zariya.

Ka ratse ta Kura ka samo baki can,
Ka komo t a Jega, ''tafo har Gaya.

Biyo har t a Sayi, ka komo t a Mangu,
Ka ratsa Dagomba, ka zo Kobiya.

Bidal dukiya wajibi ne gare mu,
Fa ko don mu kimsa zaman duniya.


Da sadaka da amre da suna da laiya ,
Sayen littafai sai akwai dukiya.

Bari da da haji da ci da marayi,
Wadannan ku san, sai akwai ajiya.

Da sa da karatu da gyaran zumunta
Da tanyon makofta f a duk, kun jiya .

Fa mun roki Allah, ya tsarshe mu tsanani
Na duniya da cuta da yunwa, tsiya .

WADATA
1 Muna soma tsari na halin wadata,
Fa jinsa da dadi cikin zuciya.

2 Mutum mawadaci akwai shi da girma,
Ana sonsa Hausa cikin zuciya.

3 Ana durkusa masa, ana bashi girma,
Ana son zumuntansa don dukiya.

4 Idan ya yi zance a taro a yarda,
Ace gaskiya ka fadi mun jiya .

5 Ku san, mawadaci ya kan kirfa karya ,
A ce babu wawa ku zo ku jiya .

6 Idan dumi nai ga taron mutane,
A kan ce, fa mai-fara'a ne shiya .

7 A ce walwala a gare shi ga duniya,
Ya kan bada labari ana dariya .

8 Idan yai karairansa , babu iyaka,
A yarda, a gyara, a ce gaskiya.

9 Fa shi ke da wayo ku san hankalinsa,
Kaman ya f i kowa cikin duniya.

Dada bambadawa suna yin yabonsa,
Suna ce, da kyawu kaman Utiya .

Ubansa wane, uwatasa wance,
Fa kakansa wane, mutanen jiya .

Da da nasa wane da 'ya tasa wance,
Da jikansa wane, fa to kun jiya.

Shi kan bada kyauta ta riga da wando
Da kurdi da tsaba har saniya.

Yana bada zanua da damma da rago,
Ya kan bada kyauta ta har godiya.

Mutum mai-wadata f a shi ke da kyauta,
Mutane su kan ce, fa ba ya shiya.

Idan ba shi zance, shina damre fuska,
Su ce, mai-kawaici, fa don gaskiya.

Su ce, ba shi zancensa, sai ya kamata,
Mutum mai-nagarta ina ya shiya ?


Diya tai dadai ba ta muni ga kowa,
A kan ce, da kyawu kaman Utiya.

A ce, doguwa ce idanu ya madara
Da fatar jiki sai ka ce maraya.

Ace tayi yatsa ya 'ya'ya na marga,
Ace ga duwawunta fa1 tsakiya .

Da mukurun barage hatsaya ta damra,
Ta sa kwandage munduwa sokiya.

Fa hannunta tafshi zama ta wadata,
Gama ba ta aikin da ya faifaya .

Idan kuwa baka ce, su kan ce, da kyawu,
Gama dai bakinta shina walkiya.

Idan kuwa fara ce, su ce, t a f i kyawu,
Farin nata koka Balarabiya.

Idan tai gajerta , su ce, babu komi,
Tana dai da kyawu, zama ta tsaya.

Gajertalta dai-dai kaman nan a ke so,
Zama tayi hanci da kan cibiya.

Idan doguwa ce, su kan ce, da kyawu,
Tsawon ya kamata, gama tai wuya.

A kan sota , mutum ya f i goma,
Ana ce, diya ce ta mai-dukiya.

Fa ga t a da nono, f a sun cika kirji ,
Idanunta kace idon hazbiya.

Kadan an y i amrenta garalta tari ,
Gama dai diya ce ta cin duniya .

A kan dauki kaya da kurdi da zanua,
A yauci gari, don a tambaya.

Mutum mawadaci akwai shi da girma,
Idan ya yi ado, sai a ce godiya.

Fa matansa, ku san, suna ba shi girma,
Suna boye sunansa don dukiya.

Suna durkusa masa, suna ba shi tur ba ,
Su ratse , suna boye fuska, jiya . "

Kadan ya cane, wanga aiki ku bar shi ,
Zama ba ni so nai , su ce, mun jiya .


36 Ku san bashi diba dukiyarsa, ya ba su
Matan nan gama dai , nufin su gare shi ajiya .

37 Fa tari talaka ya kan c i da mata,
Fa har tafi mata ta mai-dukiya.

38 Fa banza, gama babu saura a daki,
Kaman dai ruwa, an zuba rariya .

39 Kaman nan f a kyautar talaka ga mata,
Fa ko yayi , ba godiya, kun jiya?

40 Kadan dan karatu ya samu wada nan,
A kan ce da shi shaihu ne, ya iya.

41 Karatunsa dadi, rubutunsa sosai,
Hadisi, usuli duk ya biya.

42 Idan ya y i murya, a kan ce da dadi,
Kaman an y i gogen ga mai-tsagiya."

Idan an y i yunwa, mutum mawadaci
Abincinsa anberuwa, t a l i y a .

Da kaki, gurasa da waina da taushe,
Tuwo mai-fari, ga miya har miya.

Da kuskus da shashakaqq an garwaya su
Shinashir yana can cikin jar miya.

Fura kuwa ta gero a dama da nono, '
Zama dai ta safe zuma ya jiya .

Gidan mawadaci idan an gane shi ,
A kan san, wadatalsa ba tambaya.

Da soro ginane da darninsa sabo
Da shifkinsa mai-kyau f a an baibaya.


Gida na talaka kazamin gida ne
Da darni tsutsa , sai haki mai-kaya.

Da dai matsatsi da bununsa tsofo
Da kunkunniya, an dade tafaya .

Mutum mawadaci abokinsa sarki
Da malam da tsofon mutum mai-biya.

52 Mutane ku fuce matsari na waka,
Fa s h i ma talakan f a ne, kun jiya .

53 Fa na goda Allah, da na kare tsari
Na halin wada duk da halin tsiya .

54 Da tsira da girma da so duk da yarda,
Su taru ga manzo uban Rakiya.